Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar Olushegun Obasanjo ya halarci taron na ranakun asabar da lahadi, amma babu wani wakilin gwamnatin Nigeria a taron, wanda a karon farko ya sami halattar Priministan HKI Benyamin Natanyahu.
Majiyar ta bayyana cewa rashin halattar wani jami'in gwamnatin Nigeria a wannan taron ba zai rasa nasaba da halartan Priminisyan yahudawan ba. Duk da cewa duk kokarin da jaridar tayi don samun dalilan hakan bai cimma nasara.288